Bakonmu A Yau

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 1:23:38
  • More information

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Tattaunawa da Musa Idris kan saukar farashin kayayyaki a Najeriya

    19/02/2025 Duration: 03min

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3. Cikin sanarwar da ta fitar a jiya Talata, hukumar NBS ɗin ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 a watan Disambar shekarar bara ta 2024. Domin jin halin da ake ciki....la’akari da wannan rahoto, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Musa Idris daga jihar Jigawa, magidanci kuma ɗan kasuwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........

  • Dr Babangida Abdullahi na Jami'ar Baze kan ƙaruwar man da Najeriya ke haƙowa

    18/02/2025 Duration: 03min

    Kamfanin man NNPC a Najeriya ya ce sakamakon kwanciyar hankalin da aka samu, adadin man da yake hakowa kowacce rana ya karu zuwa ganga miliyan guda dubu 750, sabanin kasa da ganga miliyan guda da dubu 250 a baya. NNPC ya kuma ce yanzu haka yana hako cubic biliyan 7 na gas kowacce rana. Dangane da wannan ci gaba, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Babangida Abdullahi na Jami'ar Baze dake Abuja, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.....

  • Tattaunawa da Dr Jafar Lawal kan gazawar shugabannin Afrika a Congo

    17/02/2025 Duration: 03min

    Yayinda shugabannin ƙasashen Afrika ke kammala taronsu akan yadda za su tinƙari rikicin ƴantawayen ƙungiyar M23 a Congo, rahotanni sun bayyana nasarar da mayaƙan suka samu na sake kama Bukavu bayan birnin Goma mafi girma a lardin na Kivu. Ganin irin nasarorin da suke samu kan dakarun ƙasar ta Congo dama gazawar shugabannin Afrika wajen daƙile matsalar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Jafar Lawal, masani akan harkokin siyasar Afrika ta gabas, kuma ga yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....

  • Kabir Muhammad Baba kan sabbin harajin da aka lafta wa 'yan Nijeriya

    13/02/2025 Duration: 03min

    Ƴan Najeriya na ci gaba da gabatar da ƙorafe ƙorafe sakamakon sabbin harajin da aka ɗora musu na cire kudade a bankuna da kuma kirar waya. Kamfanonin sadarwar kasar sun sanar da karin kashi 50 na kudin kirar wayar, yayin da Babban Bankin Najeriya ya sanar da kara harajin da ake cirewa akan cirar kudi ta ATM zuwa naira 100 akan kowacce naira 20,000. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Alhaji Kabir Muhammad Baba, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai

  • Nijeriya ta samu cigaba a bangaren yaƙi da cin hanci da rashawa

    12/02/2025 Duration: 03min

    Ƙungiyar Transparency International ta fitar da rahoton ta na shekarar da ta gabata, wanda ya nuna cewar Nijeriyar ta koma matsayi na 140 daga 145 na shekarar da ta gabata , a jerin ƙasashen duniya dake fama da matsalar cin hancin.Domin tattauna wannan sabon rahoto, Bashir Ibrahim Idris ya tuntuɓ Dr. Ladan Salihu, tsohon shugaban Radiyo Nijeriya,  sai a latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.

  • Tattaunawa da Sani Rufa'i kan taron ƙasa a Nijar don komawa tubar Demokraɗiyya

    11/02/2025 Duration: 03min

    Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa kwamitin musamman da aka ɗora wa alhakin shirya taro maharawa don sake dawo da ƙasar kan turbar dimokuradiyya. Ana kyautata zaton sakamakon ayyukan kwamitin ne za su fayyace tsawon lokacin da ake buƙata don tafiyar da mulkin riƙnon ƙwarya da kuma irin salon mulin da ya kamata a ɗora Nijar a nan gaba.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sani Rufa'i ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.

  • Tattaunawa kan umarnin Tinubu ga ministocinsa na arewa don tallata ayyukansa

    10/02/2025 Duration: 03min

    A Najeriya rahotanni sun bayyana cewar yanzu haka shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin ministocinsa da suka fito daga yankin arewacin ƙasar su koma jihohin da suka fito domin kare manufofinsa da kuma bayyana irin ayyukan da yake yi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban ke ganin matsananciyar suka daga ɓangaren adawa da kuma ganin tarin barazana musamman kan salon kamun ludayin gwamnatinsa.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Harsanu Yunusa Guyaba.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.

  • Farfesa Shehu Zuru kan matakin Donald Trump na sanyawa ICC takunkumi

    07/02/2025 Duration: 03min

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin sanya takunkumi akan kotun duniya ta ICC da kuma haramtawa jami'anta dake binciken 'yan kasarsa ko kuma kawayen Amurka irin su Isra'ila. Abin tambayar shine, wanne irin tasiri wannan mataki zai yi?Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, masanin shari'a a Jami'ar Baze, da ke Nijeriya.

  • Ambasada Abubakar Cika kan kalaman Trump na ƙwace yankin Gaza

    06/02/2025 Duration: 03min

    Ƙasashen duniya sun bayyana matukar rashin amincewarsu da buƙatar shugaban Amurka Donald Trump, na ƙwace Gaza da kuma mayar da Falasdinawa wasu ƙasashe domin gina wurin shaƙatawa a ƙasarsu. Wannan matsayi ya gamu da suka daga ƙasashen duniya da dama ciki harda Majalisar Ɗinkin Duniya. Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna shirin da Ambasada Abubakar Cika, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........

  • Farfesa Abba Gambo kan tasirin dakatar da ayyukan USAID ga fannin noman Najeriya

    05/02/2025 Duration: 03min

    Ƙasashen duniya na ci gaba da bayyana damuwa dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da ayyukan hukumar USAID wadda ke taimakawa ƙasashen duniya . Wannan hukuma dai na taka gagarumar rawa a bangarori da dama a ƙasashe masu tasowa irin su Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan harkokin noma dangane da tasirin matakin a kan noman ƙasar.Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tattaunawar ta kasance....

  • Baba Ngelzarma kan yadda makiyaya ke ƙaura zuwa ƙasashe makwafta daga Najeriya

    04/02/2025 Duration: 03min

    Wasu bayanai a Najeriya na nuni da cewar sama da kaso 20 daga cikin jimillar Fulani makiyaya dake ƙasar sun yi ƙaura zuwa wasu ƙasashe makwafta, yayin da wasu ke cigaba da ƙoƙarin bin sawun ɗaukar matakin yin ƙaurar saboda matsalolin tsaro. Wasu majiyoyi sun ce hakan na faruwa ne ganin yadda makiyayan na ainahi suka faɗa tsaka mai wuya na gaba kura baya sayaki, inda a dazuka da wasu yankunan karkara suke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane, yayin da a cikin gari kuma suke faɗawa komar ‘yan sa-kai.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, Baba Usman Ngelzarma.

  • Dr Suleiman Shinkafi kan yadda ƴan bindiga ke addabar sassan jihar Zamfara

    03/02/2025 Duration: 03min

    Duk da nasarorin da sojoji ke samu kan ƴan ta’adda a arewa maso yammacin Najeriya, masu ɗauke da makaman na ci gaba da kai hare-hare a ƙauyuka da dama na jihar Zamfara. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Dr Suleiman Shu'aibu Shinkafi...

  • Mahamadou Bagadoma kan matsalolin da ƙasashen yankin Tafkin Chadi ke fuskanta

    31/01/2025 Duration: 03min

    Gwamnan jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar Brig. Gen. Mahamadou Ibrahim Bagadoma ya ce dole sai ƙasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi sun haɗe kansu idan har suna son kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi A tattaunawarsa da wakilin sashen Hausa na RFI Ahmed Abba a yayin taron gwamnonin tafkin Chadi da ke gudana a Najeriya ya ce ko kasashen na cikin ƙungiyar ECOWAS ko ba sa cikinta to ya kamata su haɗe kansu domin yaki da matsalar tsaro.

  • Akalla mutane miliyan 300 wutar zasu mori wutar lantarki-Tinubu

    30/01/2025 Duration: 03min

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa na inganta samar da wutar lantarki a fadin kasar. Tinubu ya bayyana haka ne wajen taron kasashen Afirka wanda ya tattauna yadda za'a samarwa akalla mutane miliyan 300 wutar a nahiyar baki daya. Ganin irin matsalolin wutar da ake fuskanta a Najeriya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon manajan hukumar samar da wuta a kasar, Comrade musa Ayiga, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

  • Ambasada Yusuf Tuggar kan ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS

    29/01/2025 Duration: 03min

    Tattaunawar ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar da Mohammed Sani Abubakar  kan batun cikar wa'adin ƙasashen ficewar ƙasashen AES na Mali, Burkina Faso da Nijar daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS. Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tattaunawar ta kasance...

  • Prof Peter Lassa kan zargin majalisun Najeriya da neman cin hanci daga jami'oi

    28/01/2025 Duration: 03min

    Wani bincike ya zargi kwamitin ilimi na majalisun Najeriya ta bukatar naira miliyan takwas takwas daga kowanne shugaban jami'ar tarayya kafin amincewa da kasafin kudinsu na wannan shekarar. Tuni wannan zargi ya haifar da cece kuce a cikin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Peter Lassa, tsohon shugaban hukumar gudanarwar manyan kwalejojin ilimin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...........

  • Malam Isma’il Ahmad kan buƙatar Trump na kwashe Falasɗinawa daga Gaza

    27/01/2025 Duration: 03min

    Bayan shafe watanni 15 ana gwabza mummunan yaƙi a yankin Gaza tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan Hamas da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, shugabaan Amurka, Donald Trump ya ce yaƙin ya lalata yankin na Gaza baki daya, don haka ya bayyana wa Sarki Abdallah na Jordan  buƙatar kwashe Falasɗinawa daga yankin zuwa ƙasarsa kuma ya ce ya na  sa ran tattaunawa da shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi a kan haka.  A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin lammuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya, Malam Isma’il Ahmad.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Sule Ammani kan gurfanar Obasanjo da Buhari gaban wata kotu a Faransa

    24/01/2025 Duration: 03min

    Tsoffin shugabannin Najeriya guda 2 wato Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari sun gurfana a wata kotun sasanta rikicin kwangilla domin bada ba'asi a kan soke kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ministan Obasanjo ya bayar bada saninsa ba, da kuma kin biyan kudin sasanta matsalar da gwamnatin Buhari ta ki. Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da daya daga cikin dattawan kasar Alhaji Sule Ammani,  Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyartattaunawar.

  • Dr Adamu Tilde kan faɗuwar farashin kayan abinci a Najeriya

    23/01/2025 Duration: 03min

    Rahotanni daga sassan Najeriya sun nuna cewar an samu faduwar farashin kayan abinci bayan jama'ar ƙasar suka kwashe dogon lokaci suna fama da tsadarsa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Adamu Tilde, masanin harkar noma kuma ɗan kasuwa dangane da lamarin. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........

  • Farfesa Balarabe Sani kan manufofin gwamnatin Donald Trump na Amurka

    22/01/2025 Duration: 03min

    Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikin mambobin Hukumar Lafiya ta Duniya, matakin da wasu ke ganin na iya illa ga dorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya. Dangane da tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

page 1 from 2