Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Dr Abdulhakeem Garba Funtua kan sabon wa'adin Donald Trump a Amurka
21/01/2025 Duration: 03minSabon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manufofin gwamnatinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki da ya yi a matsayin shugaba na 47. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna dangane da wadannan manufofi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Tattaunawa da Daraktan Amnesty Isa Sanusi kan yawaitar haɗarin tankar mai a Najeriya
20/01/2025 Duration: 03minƘungiyar Amnesty International ta danganta haɗrin tankin man da ya hallaka kusan mutane 100 a jihar Neja ta tsakiyar Najeriyar a matsayin talaucin da ya yiwa jama'ar ƙasar katutu, inda daraktan ƙungiyar a Najeriyar Malam Isa Sanusi ke cewa akwai buƙatar mahukunta su sassauta matakan da suke ɗauka a lamurran da suka shafi tattalin arziƙi. Matsalar ta haɗari ko kuma gobarar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya, inda ko a baya-bayan nan aka ga yadda fiye da mutane 100 suka mutu can a jihar Jigawa sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da suke tsaka da kalen man da ya malala akan titi bayan tuntsirewar wata tanka.Masana irin daraktan ƙungiyar ta Amnesty International mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Isa Sanusi na kallon talauci a matsayin babban dalilin da ke sanya mutane kai kansu ga irin wannan haɗarin wanda ke nuna buƙatar da ke akwai ga mahukunta wajen sun samar da sassauci ga jama'a don kaucewa fuskantan makamantan wannan matsaloli.Yayin wata zantawarsa da editan sashen Hausa na RFI Bashir Ibrahim I
-
Zantawa da babban Editan Jaridar Aminiya Malam Sagir Kano Saleh
17/01/2025 Duration: 02minKamar yadda aka saba a kowacce ranar Juma'a, jaridar Aminiya da ake wallafawa a Najeriya ke fita kuma Abida Shuaibu Baraza ta tattauna da Editan Jaridar Malam Sagir Kano Saleh domin jin abin da ta ƙunsa. sai latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.
-
Dokta Abdulhakim Garba Funtua kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
16/01/2025 Duration: 03minIsra'ila da kungiyar Hamas sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen yakin da suka kwashe watanni 15 suna fafatawa, wanda ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa sama da dubu 45, bayan harin da ya kashe Yahudawa sama da dubu guda. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar duniya Dr Abdulhakeem Garba Funtua game da yarjejeniyar, kuma ga yadda zantawasu ta gudana a kai.