Bakonmu A Yau

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 1:27:21
  • More information

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Hira da Kwamared Umar Hamisu Ƙofar Na’isa kan matakin ladabtar da yansanda

    17/07/2025 Duration: 03min

    Kamar yadda akaji a farkon Shirin, Hukumar kula da ƴansanda a Najeriya ta gurfanar da manyan jami’ai sama da 150 a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zarginsu da wulakanta aikin ɗansanda da kuma take hakkoki fararen hula a wasu lokutan. Bayanai sun ce an baiwa kwamitin kwanaki 10 ya gama binciken ƴansanda masu muƙamin ASP zuwa sama, ya kuma gabatar da rahoto wanda zai baiwa hukumomi damar ɗaukar matakin hukunci a kansu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar.....

  • Tattaunawa da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a Kamaru game da takarar Paul Biya

    15/07/2025 Duration: 03min

    Shugaba Paul Biya na Kamaru mai shekaru 92 ya bayyana aniyar sake tsayawa takara don neman wa'adi na 8 na mulkin ƙasar da nufin ci gaba da yiwa ƙasar hidima. Shugaba Biya ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Sai dai ko yaya jama'ar Kamaru ke kallon wannan mataki, dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Isma'ila Muhammed ɗan siyasa a ƙasar ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..

  • Tattaunawa da makusancin Buhari, Faruk Adamu Aliyu kan rasuwar tsohon shugaban

    14/07/2025 Duration: 02min

    A jiya Lahadi, 13 ga watan Yulin nan ne Allah ya yi wa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari rasuwa yana da shekaru  82 a duniya. Bayan kasancewa shugaban gwamnatin sojin Najeriya daga shekarar 1983 zuwa da 1985, ya sake dawowa a matsayin farar hula, inda ya mulki ƙasar daga shekarar 2015 zuwa 2023. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Faruk Adamu Aliyu, ɗaya daga cikin makusantan Buhari akan wannan rasuwa da irin rayuwar da yayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....

  • Tattaunawa da Alhaji Garba Suleiman Krako Madakin Saminaka kan ambaliyar Texas

    10/07/2025 Duration: 03min

    Rahotanni daga Amurka na cewa an samu ƙaruwar yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon Iftila’in Ambaliyar ruwan da ya afka wa Jihar Texas, inda zuwa yanzu adadin ya haura mutane 115, yayin da har aynzu aka gaza gano wasu aƙalla 160 da suka ɓace. Domin jin halin da ake ciki da kuma dalillan da suka haddasa aukuwar ambaliyar a Texas, Nura Ado Suleiman ya tattauna da mazaunin ƙasar ta Amurka, Alhaji Garba Suleiman Krako Madakin Saminaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....

  • Tattaunawa da Dr Idris Harbau kan taron ƙasashen BRICS a Brazil

    09/07/2025 Duration: 03min

    A ranar Litinin ƙasashe manbobin ƙungiyar BRICS suka kammala taronsu na 17 a Brazil, inda a cikin kwanaki biyu da suka shafe suna ganawa, jagororin ƙasashen suka tattauna a kan yadda manufofin shugaba Trump ke tasiri kan tattalin arziƙi da kasuwancin Duniya. Sai dai tun kafin kammala taron, shugaba Trump ɗin ya yi barazanar lafta harajin kashi 10 kan kayayyakin ƙasashen na BRICS, da ma duk wata ƙasa da ta goyi bayan matakan adawa da manufofin Amurka. Kan wannan batu, da kuma tasirin ƙungiyar ta BRICS Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziƙi da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..

  • Tattaunawa da Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW kan yawaitar haɗurra

    08/07/2025 Duration: 03min

    Rahotanni daga Najeriya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon haɗurran motoci da aka samu a ƙarshen mako cikin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da kuma jihar Oyo baya ga Lagos da kuma jihar Kogi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin hanyoyin motoci ke ci gaba da taɓarɓarewa, yayinda wasu direbobin ke tuƙi cikin yanayi na maye ko kuma saɓawa dokokin tuƙi. Dangane da wannan matsala da ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Adamu Idris Abdullahi Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW da ke Abuja ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Sai ku latsa alamar sauti don saurare.

  • Tattaunawa da Honourable Siraj Imam Ibrahim kan ambaliyar ruwan Kano

    07/07/2025 Duration: 03min

    A ƙarshen makon da ya gabata aka samu ambaliyar ruwan sama a sassan birnin Kano, a dai dai lokacin da damina ta fara kankama a jihar. Wannan matsalar ta haifar da matsaloli ga mazauna da kuma baƙin da ke zuwa birnin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon Siraj Ibrahim Imam, Kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.   Ku latsa alamar sauti son sauraron cikakkiyar Hirar.

  • Dr Aliyu Bello kan ƙawancen 'yan adawa a Najeriya

    04/07/2025 Duration: 03min

    A wannan mako ne yan adawan Najeriya suka kafa wani kawancen da suka ce zai tinkari Jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, da zummar kawar da ita daga karagar mulki. Shirin Duniyarmu Ayau na RFI Hausa ya gudanar da mahawara tsakanin Sanata Ahmed Babba Kaita na sabuwar kawancen da kuma shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Nasarawa Dr Aliyu Bello. Ga kadan daga cikin abinda shugaban APC ya fadi a cikin shirin da zai zo muku gobe da misalin karfe 5 na yamma.

  • Emmanuel Shehu kan haɗakar jam'iyyun adawa a Najeriya da nufin tunkarar APC mai mulki

    03/07/2025 Duration: 03min

    Wasu daga cikin jiga-jigan ƴan adawar Najeriya sun haɗa kansu wajen komawa jam'iyyar ADC domin shirin tunkarar gwamnatin APC mai mulki da suke zargi da rashin iya mulki, Yayin gabatar da sabbin shugabannin, ƴan adawar sun sha alwashin ceto talakan Najeriya daga halin ƙuncin da ya samu kansa. Sai dai wasu na cewa neman mulki ne kawai suke yi amma ba don talakan Najeriya ba. Bashir Ibrahim Idris ya tattauwa da shugaban cibiyar horar da ƴan Jaridu ta IIJ da ke Abuja, Dr Emman Shehu, kuma ga yadda zatawarsu ta gudanar.

  • Dr Yahuza Getso kan yadda jami'an sojoji suka hallaka Kachalla Ɗanbokolo a Zamfara

    02/07/2025 Duration: 03min

    A Najeriya mayaƙan sa kai a jihar Zamfara sun yi nasarar hallaka wasu daga cikin manyan kwamandojin ƴan bindigar da suka hana zaman lafiya a jihar, cikinsu har da Kachalla Ɗanbokolo da wasu tarin magoya bayansu. Domin sanin tasirin wannan nasara ga jama'ar yankin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauba da masanin harkar tsrao, Dr Yahuza Getso.   Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar

  • Muhammad Adamu Dansitta kan shirin gwamnatin Najeriya na dasa bishiyoyi biliyan 20

    01/07/2025 Duration: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin dasa itatuwa biliyan 20, a kokarin da take yi na magance gurgusowar hamada da tsananin zafi , har ma da sauyin yanayi. Mataimakin shugaban kasar Kashin Shetimma ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi a wajen wani taroa  kasar Habasha. Game da tasirin wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Muhammad Adamu Dansitta. Dannan alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.

  • Issof Emoud kan sabuwar Majalisar Tuntuɓa da gwamnatin sojin Nijar da kafa

    30/06/2025 Duration: 03min

    Majalisar Tuntuɓa da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa ta conseil consultatif na fara aiki a ranar Asabar 28 ga watan Yunin wannan shekara ta 2025, Majalisar mai kunshe da mambobi 194 an ɗaura mata nauyin bayar da shawarwari kan harokin da su ka shafi cigaban ƙasa da  kuma gayyato majalisa zartaswa domin amsa tambayoyi idan hakan ta kama. A kan haka Oumar Sani ya  tattauna da Hon. Issouf Emoud ɗan majalisa mai wakilta jihar Agadas.

  • Amb Abubakar Chika: cika shekaru 80 da sanya hannu kan yarjejeniyar samar da MDD

    26/06/2025 Duration: 03min

    Yau ake cika shekaru 80 da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da ta samar da Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a Birnin San Francisco da ke Amurka, a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 1945. Bikin cika shekaru 80 din na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar mai wakilai 193 ke fuskantar kalubale da dama, waɗanda suka hada da makomar ta ko kuma ci gaban tasirinta baki ɗaya. Kan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..........

  • Aliyu Dawobe kan janyewar wasu ƙungiyoyin agaji a Arewa maso Gabashin Najeriya

    25/06/2025 Duration: 03min

    Ƙungiyar agaji ta ICRC wadda ke aiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta bayyana damuwa da janyewar wasu ƙungiyoyin agaji da ke bai wa ƴan gudun hijira tallafi a yankin. Babban jami'in yada labaran ƙungiyar a Najeriya, Aliyu Dawobe da ke ziyarar aiki a Lagos, ya mana ƙarin bayani dangane da halin da suke ciki.  Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris...........

  • Janar Sani Usman Kukasheka kan rundunar tsaro ta haɗin gwiwar ƙasashen ECOWAS

    24/06/2025 Duration: 03min

    Shugabannin ƙsashen Yammacin Afrika da ke ƙarƙarshin ƙungiyar ECOWAS sun sake bayyana damuwarsu dangane da ƙruwar matsalar tsaro a yankin. Yayin taron da suka gudanar a ƙarshen mako, shugaban ƙungiyar mai barin gado kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake gabatar da buƙatarsa ta tabbatar da rundunar tsaro ta haɗin gwiwar da zata tinkari wannan matsalar. Bashir Ibrahim Idris ya tattaunawa da Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya,tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........

  • Muhammad Ibrahim Sa’id kan yunƙurin kwaso ƴan Najeriya da ke Iran

    23/06/2025 Duration: 03min

    Yanzu haka ƙasashe na ci gaba da ɗaukar matakan kwashe al’ummominsu daga Iran da kuma Isra’ila, saboda yadda yaƙi ya tsananta a tsakanin ƙasashen biyu. Bayanai na nuni da cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Iran, ya fara tsara yadda za su kwashe ƴan Najeriya da motoci zuwa Armenia kafin wataƙila a yi amafani da jiragen don dawo su gida. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muhammad Ibrahim Sa’id, ɗan Najeriya da ke karatu a birnin Qoom mai tazarar kilomita 150 a kudancin Tehran. Ku latsa alamar sauti domin jin zantawarsu........

  • IPMAN ta yaba wa Dangote na fara rarraba man fetur da Disal zuwa sassan ƙasar

    19/06/2025 Duration: 03min

    Ƙungiyar dillalan man fatir masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN ta yaba da sabon shirin matan man Dangote na fara rarraba man fetur da Disal daga Lagos zuwa sassan ƙasar, sai dai ta ci gaba da nuna damuwa kan sabon harajin naira 12,500 da gwamnatin jihar Lagos ta sanya kan duk mota guda kafin bin titin Lekki da ke kaiwa matatar Dangote da sauran kamfanonin mai dake yankin, matakin da ya haifar da fargabar samun karin faranshin litar mai, masamman a arewacin ƙasar. Sai dai a tataunawarsa da Ahmad Abba, shugaban ƙungiyar IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandi, ya ce bayan ɗan yajin aikin da derebobin dakon mai suka yi, gwamnatin Lagos ta sanya ranar Yau Alhamis, domin cimma matsaya kan wannan batu. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu................

  • Jaloud Sambo kan juya baya ga takarar Paul Biya da ƴan adawar Kamaru suka yi

    18/06/2025 Duration: 03min

    A yayin da guguwar siyasa ke kaɗawa a Jamhuriyar Kamaru, alamu na nuni da cewa jiga-jigan jam’iyyu da suka daɗe suna ƙawance da jam’iyyar MPRC  mai mulkin ƙasar za su yi wata tafiya ta daban saɓanin ta shugaba Paul Biya ba. Bisa ga dukkannin alamu, ƙusoshin ƴan siyasa daga arewacin Kamaru da suka shafe shekaru a tafiyar kuma ke riƙe da manyan makamai irin su Isa Ciroma Bakari da Bello Buba Maigari sun fara tunanin yin watsi da tafiyar shugaba Biya, kamar yadda ake raɗe-raɗi. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Jaloud Sambo, shugaban ƴaƴan jam’iyyar adawa ta MPSC da ke zaune a ƙasashen waje.......

  • Tattaunawa da Dr Awwal Abdullahi kan kashe-kashen jihar Benue

    17/06/2025 Duration: 07min

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar Benue ta tsakiya, inda rahotanni ke cewa fiye da mutane 200 ne suka mutu a wasu jerin hare-hare da aka kai Yelewata a baya-bayan nan. Kiran na zuwa bayan da daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga a Makurdi babban birnin jihar domin nuna adawa da kashe-kashen.  A tattaunarsa da Ahmed Abba, Dr. Awwal Abdullahi Aliyu, masanin harkokin tsaro, kuma babban magatakardar ƙungiyar tsoffin sojojin Najeriya, ya fara da bayyana dalilan da ke haddasa rikicin. Shiga alamar sauti domin jin cikakken bayani.....

  • Alhaji Abubakar Cika kan rikicin Isra'ila da Iran

    16/06/2025 Duration: 03min

    A wannan litinin an shiga rana ta huɗu da fara yaƙi gadan-gadan tsakanin Isra’il ta Iran, inda kowanne daga cikin ƙsashen biyu ke amfani da manyan makamai don kai wa farmaki a kan manyan biranen ƙasashensu. Domin yin dubi a game da wannan rikici da ake ganin cewa muddun ba a dakatar da shi ba zai shafar ƙasashe da dama, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon jakadan Najeriya a Iran. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hira da Ambasada Alhaji Abubukar Cika.....

page 1 from 2