Bakonmu A Yau

Mahamadou Bagadoma kan matsalolin da ƙasashen yankin Tafkin Chadi ke fuskanta

Informações:

Synopsis

Gwamnan jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar Brig. Gen. Mahamadou Ibrahim Bagadoma ya ce dole sai ƙasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi sun haɗe kansu idan har suna son kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi A tattaunawarsa da wakilin sashen Hausa na RFI Ahmed Abba a yayin taron gwamnonin tafkin Chadi da ke gudana a Najeriya ya ce ko kasashen na cikin ƙungiyar ECOWAS ko ba sa cikinta to ya kamata su haɗe kansu domin yaki da matsalar tsaro.