Bakonmu A Yau

Baba Ngelzarma kan yadda makiyaya ke ƙaura zuwa ƙasashe makwafta daga Najeriya

Informações:

Synopsis

Wasu bayanai a Najeriya na nuni da cewar sama da kaso 20 daga cikin jimillar Fulani makiyaya dake ƙasar sun yi ƙaura zuwa wasu ƙasashe makwafta, yayin da wasu ke cigaba da ƙoƙarin bin sawun ɗaukar matakin yin ƙaurar saboda matsalolin tsaro. Wasu majiyoyi sun ce hakan na faruwa ne ganin yadda makiyayan na ainahi suka faɗa tsaka mai wuya na gaba kura baya sayaki, inda a dazuka da wasu yankunan karkara suke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane, yayin da a cikin gari kuma suke faɗawa komar ‘yan sa-kai.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, Baba Usman Ngelzarma.