Tambaya Da Amsa

Shirin Sallah na musamman akan muhimmancin azumi ga musulmi

Informações:

Synopsis

Kasancewar Azumin na watan Ramadan ya kunshi ladubba da tarin alkhairi a cikinsa, waɗanda suka haɗa ƙara kusanci ga mahalicci ta hanyar gudanar da ɗumbin ibadu da kyautatawa juna da nisantar dukkanin ayyuka ko lamura da suka saɓawa shari’a. Watan na Ramadan wata ne mai matuƙar daraja wanda dukkanin musulmi ke neman falala daga Allah a cikinsa, wakimmu na jihar Bauchi a Najeriya Ibrahim Malam goje ya zanta da Shehin Malami Imam Muhammad Hadi Abubakar, Na'ibin Babban Limamin Masallacin Juma'a na At-Taqwa, da ke garin Bauchi dangane da muhimmancin watan na Ramadana.