Lafiya Jari Ce

Lafiya Jari Ce: Illar rashin zuwa awon ciki ga lafiyar mata da jariransu

Informações:

Synopsis

Shirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta’azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri. Ƙorafe-ƙorafen jami’an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala’alla ake ganin ta na da alaƙa ta ƙut da ƙut da halin matsi ko kuma tsadar rayuwar da ake fama da ita wadda ta ƙai ƙololuwa a yankin arewacin Najeriya mai fama da durƙushewar ɓangaren kiwon lafiya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.