Synopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodes
-
Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jere
20/05/2024 Duration: 10minShirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere.
-
Har yanzu akwai rashin tabbas game samar da ingantaccen tsaro yayin gasar Olymics mai zuwa
06/05/2024 Duration: 09minShirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
-
Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana
22/04/2024 Duration: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana. A yanzu Bayern Munich zata fafata da Real Madrid ita kuwa Borussia Dortmund ta kara Paris Saint-Germain.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
-
Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila
15/04/2024 Duration: 09minShirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.