Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan matakin Nijar na hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare
15/05/2025 Duration: 10minMakonni kaɗan gabanin bukukuwan Sallar Layyah, mahukuntan jamhuriyar Nijar sun bayar da umurnin hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare. Ga alama dai an ɗauki matakin ne don hana tashin farashin dabbobi a wannan lokaci, yayin da wasu ke cewa matakin zai iya cutar da tattalin arzikin ƙasar.Abin tambayar shine, menene amfani ko kuma illar wannan mataki ga ƙasar?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan yadda ƴanbindiga suka tsananta kai hare-hare
14/05/2025 Duration: 09minHare-haren ƴanbindiga na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Najeriya, inda a baya-bayan nan suka tsananta kai farmaki hatta akan sansanonin soji, kusan a iya cewa haka take a sauran yankin sahel musamman Burkina Faso, lamarin da kanyi sanadin mutuwar jami’an tsaro masu tarin yawa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan wannan maudu'in.......
-
Ra'ayoyi kan kula da lafiyar kwakwaluwa
13/05/2025 Duration: 10minShin ko kun san muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa kuwa? Wannan tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, lura da cewa yanzu haka akwai ɗimɓin mutane da ke fama da wannan matsala a sassan duniya. Yayin da wasu ke kira wannan lalura a matsayin hauka, masana kuwa na cewa hatta shiga yanayi na damuwa ko da ƙuncin rayuwa na iya haddasa wannan matsalar.Shin ko wace irin kulawa ku ke bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
09/05/2025 Duration: 10minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...