Synopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodes
-
Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya
17/12/2024 Duration: 09minShirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
-
UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al’adun duniya
10/12/2024 Duration: 10minShirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa. Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
-
Gushewar al'adar tatsuniya a cikin al'ummar Hausawa
26/11/2024 Duration: 10minShirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.
-
Tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Nassarawa a Najeriya
21/11/2024 Duration: 09minA yau shirin al’adun zai je jihar Nassarawa inda muka samu zantawa da mai Martaba Sarkin Nassarawa,daga bisani za mu je Jamhuriyar Nijar inda zamu duba koma bayan wakokin gargajiya a cikin al’umma.
-
Masarautar Keffi a cikin shirin Al'adun mu
17/11/2024 Duration: 10minYau shekaru tara kenan da zama Sarkin masarautar keffi da mai martaba Dr alhaji shehu usman chindo yamusa,bayan rasuwar mahaifinsa mai martaba alhaji Chindo Yamusa na uku 3.A cikin shirin al'adu za ku ji tarihin Sarkin na Keffi.
-
Tasirin al'adun gargajiya wajen tafiyar da mulki bayan ficewar turawa
06/11/2024 Duration: 10minShirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma. A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
-
Yadda bikin baje kolin cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery da ke Lagos ya gudana
29/10/2024 Duration: 09minShirin al'adunmu na gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gagarumin biki baje kolin al'adu a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. An gudanar da bikin ne a fitacciyar cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery, wanda ya shahara a duniya, bikin ya tattaro mutane da dama daga sassan fasaha, kasuwanci, siyasa da diflomasiyya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aboulaye Issa........
-
Yadda al'adar gaɗa ke shirin gushewa a tsakanin al'ummar Hausawa
22/10/2024 Duration: 09minShirin al'adunmu na gado tare da Aboulaye Issa, ya mayar da hankali ne kan al'adar gaɗa da ke ƙoƙarin gushewa tsakanin al'ummar Hausawa duk da tasirinta a shekarun baya musamman tsakanin matasa.
-
Sarkin Damagaram ya naɗa ɗan Najeriya a matsayin Talban masarautarsa
08/10/2024 Duration: 09minShirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
-
Yadda aka gudanar da bikin Sallar Gani a Najeriya da Nijar
01/10/2024 Duration: 10minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al’adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
-
Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa
17/09/2024 Duration: 09minShirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
-
Jerin shirye-shirye kan tarihin zaman takewar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa
10/09/2024 Duration: 09minShirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
-
Yaya tsarin tafiyar da mulki yake a ƙasar Hausa kafin zuwan turawa
27/08/2024 Duration: 09minShirin na wannan mako ya duba irin tasirin masu mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan turawan Mulkin mallaka Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani
-
Yadda sana'ar ƙira ke gushewar a al'adar ƙasar Hausa
13/08/2024 Duration: 09minA yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana’o’i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.
-
Yadda Kabila Berum a Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'ada
30/07/2024 Duration: 09minA wanan makon shirin ya mayer da hankali ne kan yadda kabilar Berum da ke jihar Plateau ta tarayyar Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'ada. Kuna iya latsa alamar sautin domin sauraren cikakken shirin.....
-
Shirin ya mayar da hankali kan Kabilar Gwari a Najeriya
23/07/2024 Duration: 10minShirin na wannan mako zai yi duba ne kan Kabilar Gwari da ake samun su a tsakiyar Najeriya. Kabilar Gwari da bahaushe ke kira da "Gwarawa" na da al'adu daban-daban masu ban mamaki da suka sha banban da sauran kabilun mutanen da ke kewaye da su.Domin jin cikakken shirin dannan alamar saurare tare da Abdullahi Isa
-
Shirin yayi waiwaye kan rayuwar fitaccen makadin gargajiya marigayi Alhaji Ali na Maliki
09/07/2024 Duration: 09minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa.
-
Yadda al'ummar Wemawe na Benin ke shirya bikin al'adunsu a duk shekara
02/07/2024 Duration: 09minShirin al'adun gargajiya na wannan mako, ya je jamhuriyar Benin musaman yankin Wemewe, inda ƙabilar yankin ke shirya wani ƙasaitaccen bikin nuna al’adunsu a duk shekara, wadda ke ƙarfafa danƙon zumunci tsakaninsu da sauren ƙabilu. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
-
Irin rawar da masarautu ke takawa wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata kashi na 2
11/06/2024 Duration: 09minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ci gaba ne akan na makon daya gabata wanda ya duba muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. inda shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
-
Irin rawar da ya kamata masarautu su taka wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata
04/06/2024 Duration: 10minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........