Ilimi Hasken Rayuwa

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:48:18
  • More information

Informações:

Synopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodes

  • Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu

    30/07/2024 Duration: 09min

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji. A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

  • Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana

    23/07/2024 Duration: 09min

    Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.

  • Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya

    16/07/2024 Duration: 10min

    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...

page 2 from 2