Dandalin Fasahar Fina-finai

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 8:00:20
  • More information

Informações:

Synopsis

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodes

  • Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube

    18/07/2021 Duration: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.

  • Dandalin Fasahar Fina-Finai: Ta'aziyyar jaruma Zainab Booth

    11/07/2021 Duration: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, Hauwa Kabir ta kawo ta'aziyyar jarumar Kannywood da Allah ya wa rasuwa a makon da ya gabata,inda ta tattauna da abokan aikinta na Kannywood. Shirin ya kuma leka Nollywood da Bollywood.

  • Jarumai mata na fuskantar kalubale daga masu kallo a kafafen sada zumunta

    27/06/2021 Duration: 20min

    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan yadda Jarumai musamman mata a musamman a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood ke fuskantar cin zarafi daga masu kallo a kafafen sada zumunta na zamani.

  • Rayuwar mawaka a Duniyar yan fim a Najeriya

    20/06/2021 Duration: 20min

    Mawaka fina-finai a Najeriya na rayuwa ba tareda sun ci moriyar aikin da suke yi ba,banda haka Hawa ta samu tattaunawa da Haro mawakin hausa a Kaduna dake Najeriya.A cikin shirin Duniyar Fina-finai tareda Hawa Kabir,ta samu tattaunwa da wasu dake ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya.Hawa Kabir ta samu

page 2 from 2